Ɗaruruwan mutane sun fito zanga-zanga a birnin tarayya Abuja (Hotuna)
A ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 masu zanga-zanga sun fito ƙwansu da ƙwarƙwatansu, domin nuna fushin su da damuwa akan talauci da rashin tsaron da yake damunsu.
A babban birnin tarayya Abuja, mata da dama sun fito har da tsofaffi domin yin wannan zanga-zangar.
“An kashe mana mazaje, an barmu da marayu, ga yunwa, ina fama da rashin lafiya amma na fito dan yin wannan zanga-zangar lumana” in ji wata mata.
KU KUMA KARANTA: An tarwatsa masu zanga-zanga kan ƙoƙarin kunna wuta a ƙofar gidan gwamnatin Kano
Wakilin Neptune Hausa, Abubakar Kado, ya ɗauko mana rahoton cewa ana jefa borkonon tsohuwa, wato “tear gas” a yayin zanga-zangar.
‘Yan zanga-zangar na cewa su koma baya saboda kar borkonon tsohuwar ta same su.
Kalli hotunan Zanga-zangar a nan: