Ɗan takarar jam’iyyar adawa Bassirou na kan gaba a zaɓen Senegal

0
141

Sakamakon farko-farko da ke fitowa dangane da zaɓen Senegal na nuna cewa Bassirou Diomaye Faye ke kan gaba a zaɓen inda ake ganin zai iya samun ƙuri’u mafi rinjaye, sai dai abokin hamayyarsa da ke jam’iyya mai mulki ya ce akwai buƙatar a je zaɓe zagaye na biyu domin tantance wanda ya ci zaɓen.

Tun a ranar Lahadi magoya bayan jam’iyyar adawa suka soma murna a kan titunan Dakar babban birnin ƙasar bayan kafafen watsa labaran ƙasar sun soma sanar da sakamakon rumfunan zaɓe waɗanda suka nuna cewa Faye mai shekara 44 na kan gaban babban abokin hamayyarsa Amadou ba.

Akwai ƴan takara da dama na shugaban ƙasar waɗanda tun a ranar Lahadin suka amince da shan kaye a zaɓen.

KU KUMA KARANTA: Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Senegal ranar 24 ga watan Maris

Ana sa ran za a sa ran za sanar da sakamakon zaɓen a ranar Juma’a mai zuwa.

Mutane da dama na fatan zaɓen zai kawo zaman lafiya da haɓakar tattalin arziƙi a ƙasar bayan an shafe kusan shekara uku ana samun cikas a fagen siyasa a ƙasar.

Amadou Ba, shi ne ɗan takarar da Shugaba Macky Sall yake goya wa baya wanda zai sauka daga mulkin ƙasar a daidai lokacin da soyayyarsa ga mutane ta ragu bayan ya shafe wa’adi biyu kan mulki.

Leave a Reply