Ɗan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya harbe kansa

Wani ɗan sanda mai muƙamin Sufeto ya kashe abokin aikinsa sannan ya harbe kansa har lahira.

Wannan ƙarar kwana ya faru ne ranar Lahadi a ƙauyen Nyogor-Lueku, ƙaramar Hukumar, Jihar Ribas.

Aminiya ta samu bayani cewa ’yan sandan biyu suna aiki ne a caji ofis da ke Taabaa, lokacin da suka tafi aiki Nyogor-Lueku su kamo wani mutum bisa wasu tuhume-tuhume da mahaifiyarsa ta kawo ƙara ofishin.

Kazalika ana zargin sa da bijire wa umarnin gayyatar da aka yi masa, al’amarin da ya kawo ce-ce-ku-ce tsakaninsa da jami’an.

Majiyar labarinmu ta ce “Ana tsaka da wannan cacar baka sai cikin kuskure Sufeto Nelson Abuante ya yi harbi ya samu abokin aikinsa Gbaramana, ya ji mummunan rauni

“A sakamakon haka sai Abuante da mahaifiyar mutum da aka je ƙara suka gaggauta ɗaukar sa zuwa asibiti a cikin mota, amma sai mai ya kare a hanya, ta wannan dalili me Sufeto Monday ya ce ga garin ku nan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Gwambe, sun kama matashin da ya kashe wata mata mai shekaru 58

“Har-wa-yau ganin abokin aikinsa ya mutu, shi ma Sufeto Abuante ba tare da jinkiri ba ya sanya bindigarsa ya harbe kansa.”

Wakilin mu ya tuntuɓi kakakin rundunar Grace Iringe-Koko, kuma ta tabbatar da hakan ya afku, ta kara da cewa “An kafa kwamitin bincike a kan lamarin.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *