Ɗan majalisar wakilai na NNPP da tirabunal ta kora, ya ƙwato kujerarsa a kotun ƙoli

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar mazaɓar Tarauni a Jihar Kano, Mukhtar Umar Yarima, ya ƙwato kujerarsa a Kotun Ƙoli a ranar Asabar.

Tun a watan Agusta ne Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen majalisar jiha da ta tarayya ta ce zaɓen Yarima ba halastacce ba ne.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a, I.P. Chima ce ta haramta zaɓen na Yarima sakamakon aikawa da takardun karatun makarantar firamare na jabu ga hukumar zaɓe ta INEC.

Amma sai kotun ƙolin ta ƙi amincewa da hukuncin tirabunal ɗin, inda ta ce ta gaza tabbatar da laifin amfani da takardun jabu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *