No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mayakin ƙungiyar Boko Haram ya mika wuya ga sojojin Operation Haɗin Kai da ke Jihar Borno.

Dan ta’addan da ya fito daga sansanin Boko Haram da ke Dajin Sambisa ya mika wuya ne ga sojojin Bataliya ta 112 da ke Mafa a ranar 28 ga Afrilu, 2024.

Hakazalika ya mika wa sojojin bindigarsa ƙirar Ak47 da alburusai da wayoyin salula uku da sauran kayayyaki.

KU KUMA KARANTA: Rashin tsugunar da ‘yan Boko Haram da suka miƙa wuya babban haɗari ne- Barista Bulama Bukarti

Daga lokaci zuwa lokaci dai akan samu mayakan Boko Haram da ke miƙa kansu ga sojojin Najeriya sakamakon matsa wa sansanoninsu da sojoji ke  yi da luguden wuta.

Rikicin Boko Haram dai ya laƙume rayuka da dama, musamman a jihohin Borno da Adamawa da Vobe, gami da raba dubban daruruwan jama’a da muhallansu.

Har yanzu dubban ɗaruruwan muta da rikicin ya daidaita suna zaune a sansanoni gudun hijira, wasunsu ma a kasashen waje, wasu kuma sun bar mahaifansu.

Har yanzu ɗaruruwan mutane da suka haɗa da mata da ƙananan yara da ƙungiyar ta yi garkuwa da su ba su dawo ba.

A shekarar 2009 ƙungiyar Boko Haram ta fara tayar da ƙayar baya, kuma har yanzu ba a shawo kan masalar ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...