Ɗan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Najeriya, Aliko Ɗangote, a matsayin wanda ya fi kuɗi a nahiyar Afirka.
Sabon jadawalin attajiran da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Ɗangote ya sauko daga matsayin ne bayan dala biliyan $3.8bn sun ragu daga cikin arzikinsa.
Mujallar ta ce arzikin Dangote ya koma dala biliyan $9.7 a watan Janairun shekarar 2024, yayin da arzikin Johann Rupert dan kasar Afirka ta Kudu ya koma dala biliyan 10 a cikin watan Janairun shekarar 2024.
Duk da cewar shi ma attajirin Afirka ta Kudun ya rasa dala miliyan $700m cikin arzikin nasa, shi ne ya fi arziki a nahiyar Afirka, in ji mujallar ta Forbes.
Johann Rupert mai shekara 73 dai shi ne shugaban kamfanin kayan alatu na Compagnie Fiannciere Richemonte da ke ƙasar Switzerland.
KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu
Kazalika Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, ya koma attajiri na shida da ya fi kuɗi a Afirka daga matsayi na huɗu da yake a baya, in ji mujallar Forbes.
Shi kuma Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, ya koma na 10 daga matsayi na shida a jerin attajiran da suka fi kuɗi a Afirka.
Ana ganin karyewar darajar naira da darajar kuɗin Rand na Afirka ta Kudu ya taka rawa wajen rage yawan arzikin attajiran na Afirka a rahoton mujallar Forbes.