Ɓarayi sun sace kayan cikin Taransifoma a GGSS Jogana da ke Kano

0
202
Ɓarayi sun sace kayan cikin Taransifoma GGSS Jogana da ke Kano

Ɓarayi sun sace kayan cikin Taransifoma a GGSS Jogana da ke Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugabar Makarantar, Hajiya Lariya Balarabe Wudil ta bayyana damuwarta kan rashin ingataccen tsaro da Makarantar ke fama dashi sakamakon faduwar wani sashi na kantangar Makarantar ga kuma tsufa daya cimma masu gadin Makarantar.

‎Ta bayanna hakan ne yayin wata Ziyara da Zannan Kano, Alhaji Abdulkadir Ma’aji kuma Hakimin Jogana yakai Makarantar a Alhamis dinnan.

KU KUMA KARANTA: Bai kamata a dinga bai wa ɓarayi muƙamin Ministoci ba – Sarki Sanusi

‎Malama Lariya ta kuma bukaci Gwamnatin Jiha da ta maida Makarantar ta kwana ganin yadda suke da dumbin dalibai Mata.

‎Zannan Kano, Alhaji Abdulkadir Ma’aji ya bata tabbacin kai dukkanin kokenta zuwa gaba dan daga Likkafar Makarantar da kuma samar da tsaro dama kawo karshen matsalar Lantarki da suke fama da ita.

Leave a Reply