Ƴan sanda sun tarwatsa ƙungiyar ‘yan fashi a Jigawa

5
686

Rundunar ‘yan sanda ta kama wata ƙungiyar ‘yan fashi da makami a Jigawa tare da cafke wasu mutane biyu da ake zargi.

Wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, Lawal Shiisu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Ringim.

“A ranar 2 ga watan Yuni, 2023 da misalin ƙarfe 19:30, an sanar da tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen Ringim, waɗanda ke aiki bisa ga bayanan sirri game da wasu ƙwararrun ‘yan fashi da makami.

“Sun kammala mugunyar shirinsu na ficewa don yin wani mummunan aiki a kan titin Wudil da Garko a jihar Kano.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun mamaye gidan Matawalle, sun ƙwato motoci sama da 40

“Tawagar ‘yan sanda da ’yan banga sun kai farmaki inda suka kama Hamza Abdullahi mai shekaru 22 (wanda aka fi sani da Chumo) mazaunin Fulani na Wangara a yankin Ringim.

“Haka kuma an kama wani Hassan Ya’u mai shekaru 25 a ƙauyen Tsoma Fulani dake yankin Ajingi a jihar Kano, ɗauke da wata ƙaramar bindiga ƙirar revolver guda ɗaya da babura guda biyu.”

Shiisu ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun tare hanyar Dunduɓus zuwa Gamoji ne a ranar 6 ga watan Mayu, inda suka yi watsi da babura biyu da suka ga ‘yan sanda.

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun kuma amsa laifin yin fashi da makami a kan titin Gujungu-Miga, titin Kiyawa-Shuwarin, da Fanisau-Kano, duk a Jigawa.

Ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan, Emmanuel Ekot, ya yabawa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke ba su, ya kuma buƙace su da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani don magance masu aikata laifuka.

5 COMMENTS

Leave a Reply