Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da ba a san adadinsu ba da ke tafiya a kan hanyar East-West a Ugheli, jihar Delta da ke kudu maso-kudancin Najeriya.
Direban motar ya ranta a na kare ba tare da samun ko rauni ba. Kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Delta Edafe Bright ya bayyana cewa wataƙila fasinjojin cikin motar ɗalibai ne da ke dawowa daga makarantarsu a Calabar, Jihar Cross River ranar Juma’a da daddare, kafin a yi garkuwar da su a ƙaramar motar bas da suke ciki.
Ya ce ya zuwa yanzu ba a buƙaci a biya kuɗin fansa ba. Sai dai kuma, ƴan sanda sun bazama neman mutanen da suka yi garkuwa da ɗaliban.
“Hedkwatar ƴan sanda na sane da wannan mummunan al’amari, kuma muna yin duk mai yiwuwa don tabbatar da an kuɓutar da su ba tare da wata matsala ba,” in ji Bright a saƙon da ya wallafa a shafin X.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindigar da suka sace ɗalibai 286 sun buƙaci kuɗin fansa naira biliyan ɗaya
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami’a da dama a jihar Cross River mai maƙwabtaka.
A Najeriya, ƴan bindiga na yawan garkuwa da ɗalibai a makarantunsu tare da neman kuɗaɗen fansa kafin su sako su, lamarin da ke ƙara ta’azzara sha’anin tsaro a ƙasar.