Ƙungiyar ƙwadago ta ba wa gwamnoni wa’adi kan mafi ƙarancin albashin jihohinsu

0
231

Ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnonin jihohi wa’adin mako biyu su fara tattaunawa kan batun biyan ƙarancin albashin Naira 35,000 ga ma’aikata a jihohinsu.

Wannan wa’adin ya yi daidai da sharuɗɗan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya, da ƙungiyoyin ƙwadago ta Najeriya suka sanya wa hannu.

Sassan Jihohin ƙungiyoyin ƙwadagon sun ba da wa’adin makonni biyu inda suka tuntuɓi gwamnonin da su hanzarta aiwatar da shirin biyan ƙarancin albashin.

A wani labarin kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi naira tiriliyan 1 da nufin taimakawa gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin tattalin arziƙin da ake samu na cire tallafin man fetur.

KU KUMA KARANTA: Za mu sake duba biyan albashin ma’aikatan gwamnati – Tinubu ga shugaban bankin duniya

A ƙarkashin wannan shirin, kowane magidanci zai karɓi Naira 25,000 na tsawon watanni uku, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.13.

Ministar ma’aikatar jin ƙai, Dakta Betta Edu, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 61 ne za su ci gajiyar wannan tallafin kuɗi.

A baya dai shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta tanadi cewa duk ma’aikatan tarayya za su karɓi ƙarancin albashin naira 35,000 daga watan Satumba, har sai an kammala sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Leave a Reply