Ƙungiyar NLC ta gudanar da zanga-zanga, saboda tsadar rayuwa a faɗin Najeriya

Mambobin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya wato (NLC) sun gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar sakamakon matsin rayuwa, yunwa da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a ƙasar.

Zangar-zangar na zuwa ne biyo bayan da ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayyar ƙasar suka gana a jiya Litinin, a wani mataki na kawo tsayar da zanga-zangar, amma taron ya ƙare ba tare da an cimma matsaya ba tsakanin ɓangarorin biyu.

Tun da misalin ƙarfe 7 na safe ne mambobin ƙungiyar ta NLC suka fara taruwa a sassa daban-daban na Najeriya, ɗauke da kawalaye mai ɗauke da mabambantan saƙonni da kuma sanya tufaffi mai tambarin ƙungiyar NLC.

Saƙonnin mabambanta dake kan kwalayen da mambobin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya suka riƙe sun haɗa da ”a kawo ƙarshen yunwa da matsin tattalin arziƙi a ƙasar”, ”gwamnati ta sake salo wajen sauraron koken al’umma ganin yadda talaka baya iya samun abinci”, “a yau ana sayar da buredi a kan naira 150”.

A birnin tarayya Abuja, mambobin ƙungiyar NLC sun taru a harabar hedikwatar ƙungiyar dake unguwar Central Area sannan suka fara tattakin zangar-zangar daga nan har zuwa majalisun tarayyar Ƙasar.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwana biyu kan cire tallafin mai

Mambobin ƙungiyar NLC sun taru a harabar hedikwatar ƙungiyar dake unguwar Central Area.

A jihar Neja dake maƙwabtaka da birnin tarayya Abuja, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a jihar ne ya jagoranci mambobinta zuwa harabar majalisar dokokin jihar sakamakon halin matsin rayuwa da ‘yan ƙasa ke ciki da kuma yadda mambobin ƙungiyar ke ci gaba da kokawa kan mummunar tasirin da hare-haren ‘yan bindiga da sauran miyagu ke yi ga matsalar yunwa da ake ciki.

A wani ɓangare kuma wasu ‘yan Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar kare haƙƙin fararen hula wato Network of Civil Society for Accountability sun fito zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Bola Tinubu inda suka riƙe takarda mai mabambantan saƙonni kamar “dole ne mu yi haƙuri da Shugaban Ƙasa, mu ba shi lokaci don kawo sauyin da ake buƙata.

Ƙungiyar NLC dai na zanga-zangar nuna halin matsin da ake ciki a ƙasar na yini biyu don farkar da gwamnati a kan nauyin da ya rataya a wuyanta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *