No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ƙungiyar Liverpool ta samu tazarar maki 8 akan teburin gasar Firimiya

Mohamed Salah ya taimaka wa Liverpool wajen samun tazarar maki takwas a saman teburin Firimiyar Ingila bayan ya ci kwallaye biyu a nasarar 3-2 da suka samu kan Southampton a yau Lahadi.

Liverpool ta yi nasara ne bayan Salah ya farke ƙwallon farko a minti na 65, sannan ya ci bugun fanareti a minti na 83 bayan hannun Yukinari Sugawara ya taba ƙwallo a cikin gida.

Dominik Szoboszlai ya fara ci wa Liverpool ƙwallo daga wani sakacin da Southampton ta yi, amma Southampton ta farke bayan Adam Armstrong ya ci bugun fanareti a minti na 42 sannan ya taimaka wa Mateus Fernandes da ya ci kwallo a minti na 56, kafin Salah ya sake ba Liverpool nasara.

Wannan nasara ta nuna ƙarfin Liverpool a kakar bana, yayin da Salah ya kai kwallaye 10 a gasar bana, yana biye da Erling Haaland na Manchester City, wanda ke da 12.

KU KUMA KARANTA: Liverpool ta lallasa Manchester United ci 3 da nema

Dominik Szoboszlai ya ce Liverpool za ta ci gaba da mai da hankali kan gasar ba tare da duban matsayi na sauran ƙungiyoyinba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...