Ƙungiyar Chelsea za ta bar buga wasa a Stamford Bridge

0
58
Ƙungiyar Chelsea za ta bar buga wasa a Stamford Bridge

Ƙungiyar Chelsea za ta bar buga wasa a Stamford Bridge

Mahukuntan ƙungiyar Chelsea ta Ingila sun fara tattaunawa kan shirin gina sabon filin wasa da zai ƙara yawan mutanen da za su iya shiga kallon wasa daga 42,000, adadin da filin Stamford Bridge yake ɗauka a yanzu.

Wannan mataki zai tilasta wa Chelsea yin ƙaura daga sanannen filin wasanta na Stamford Bridge, inda za ta koma unguwar Earl’s Court da ke lardin Kensington na birnin London.

Rahotanni daga jaridar The Guardian sun ce mahukuntan ƙungiyar sun yi wata tattaunawa da hukumar Sufuri ta London, da kuma kamfanin gine-gine na Delancey kan yiwuwar komawa da mazaunin Chelsea zuwa Earl’s Court.

Chelsea ta ƙuduri aniyar ƙara girman filinta daga fili mai cin mutane 42,000, amma ta gaza cim ma wani cigaba wajen ƙara girman filin zuwa yanzu.

Wannan ne ya saka Chelsea ta fara neman wani wuri yanki a birnin London, inda za ta gina filin wasa sabo fil. An ƙiyasta cewa sabon wurin da ke Earl’s Court zai ci wa Chelsea kusan fam miliyan £500 (dala miliyan $653).

KU KUMA KARANTA: Drogba, Obi Mikel sun shawarci Victor Osimhen ya tafi Chelsea

Chelsea ta fuskanci matsaloli ne wajen ƙara girman Stamford Bridge, sakamakon kusancin filin da layin dogo na ƙarƙashin ƙasa. Wannan ne ya sa ta ɗauki wannan zaɓi mai matuƙar ƙalubale.

Sai dai kasancewar Stamford Bridge tana mallakin kamfanin Chelsea Pitch Owners, kamfanin zai iya kawo tarnaƙi kan wannan yunƙuri.

Haka nan Chelsea za ta iya samun matsala da hukumar kula da gine-gine ta Earl’s Court, wato ECDC, wadda aka ce ba ta da shirin shigar da batun gina sitadiyam a yankin.

Bugu da ƙari shirin na Chelsea zai iya tayar da taƙaddama tsakanin mamallaka ƙungiyar, wato attajiri Todd Boehly da kamfanin Clearlake Capital, wanda kowannensu ke ƙoƙarin karɓe hannun jarin ɗayan.

Leave a Reply