Ƙirƙirar jihohi ba zai yiwu a yanzu ba – Majalisar Dattawa

0
191
Ƙirƙirar jihohi ba zai yiwu a yanzu ba - Majalisar Dattawa

Ƙirƙirar jihohi ba zai yiwu a yanzu ba – Majalisar Dattawa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kakakin majalisar dattawa ta goma, Yemi Adaramodu, ya ce a halin yanzu ba za a iya ba da shawarar ƙirƙirar kowace jiha ba. Ya bayyana haka ne a Ilawe Ekiti a ƙarshen mako, inda ya ce majalisar ta karɓi shawarwari 61 na ƙirƙirar jihohi daga dukkan shiyyoyi, amma tsarin na buƙatar cikakken duba bayanan ƙididdiga, yanayin ƙasa da tarihi.

Adaramodu ya ce irin wannan buƙata ana tattaunawa ne a lokacin bitar kundin tsarin mulki, tare da jin ra’ayin jama’a da sauran masu ruwa da tsaki.

KU KUMA KARANTA: Za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi 19 a faɗin Najeriya – Gwamnatin tarayya 

Ya kara da cewa kwamitin bitar kundin tsarin mulki ƙarƙashin Barau Jibrin zai tantance buƙatun kafin a gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a.

A cewarsa, har yanzu babu wata jiha da aka amince za a ƙirƙira, kuma ba za a yanke hukunci ba sai bayan an kammala tattaunawa da rahoton ƙarshe.

Leave a Reply