‘Ƙawancen Nijar, Mali da Burkina Faso zai zama na har abada’

0
146

Firaiministocin Nijar da Burkina Faso da Mali ranar Asabar sun jaddada matsayarsu ta samun makoma iri ɗaya ƙarƙashin ƙawancen da ya nesanta su da galibin ƙasashen Yammacin Afirka tun bayan da aka yi juyin mulki a ƙasashen.

Sojoji ne suke mulkar ƙasashen uku bayan da suka kifar da gwamnatocin farar-hula da aka soma a 2020. Hakan ya sanya ba sa jituwa da galibin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS, waɗanda suke ƙira a gare su da su mika mulki a hannun gwamnatocin dimokuraɗiyya.

“Daga yanzu, muna cewa, idan kai ɗan ƙasar Mali ne ko Nijar ko kuma Burkina, makomarmu ɗaya ce. Za mu kasance tare,” a cewar firimiyan Burkina Faso Appolinaire Joachim Kyelem de Tambela a wani taron manema labarai da suka gudanar a Yamai, babban birnin Nijar.

“Makomarmu tana hannayensu,” in ji shi.

Kwana guda kafin haka, Firaiministocin uku sun gabatar da jawabi a gaban dubban jama’a da ke murnar ficewar dakarun Faransa daga Jamhuriyar Nijar.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci

Dukkan ƙasashen uku sun raba gari da Faransa, wadda ita ce tsohuwar uwar goyonsu, matakin da ya karya tasirin da take da shi a yankin Sahel da kuma yin illa ga yunƙurin ƙasashen duniya na kakkaɓe masu tayar da ƙayar baya da ke yankin.

A wani mataki da ke nuna cewa sun samu ‘yanci daga Faransa da ECOWAS, ƙasashen uku sun yanke shawarar haɗa gwiwa a fannin tsaro da siyasa da tattalin arziki inda suka kafa ƙungiyar Ƙawancen Sahel (AES).

“Mun kafa ƙungiyar AES. Idan kuka lura, komai ya fara da batun tsaro. A yau, haɗin kai tsakanin sojojin ƙasashen uku ya kai mataki babba. Kuma hakan ya tsorata wasu mutane,” in ji Firaiministan Mali Choguel Maiga.

A watan Agusta, cibiyar ACLED ta Amurka wadda ke nazari kan tsaro ta ce bincikenta ya gano an samu ƙaruwar tashe-tashen hankula a Mali da Burkina Faso tun bayan da sojoji suka kwace mulki.

Ƙasashen ba su yi cikakken bayani game da yadda ƙawancen nasu zai kasance ba, amma firaiministan Nijar Ali Lamine Zeine ya ce nan gaba duka ƙasashen za su rika ɗaukar mataki iri ɗaya kan batutuwan da suka shafe su.

Leave a Reply