Ƙasashen duniya sun ba mu kunya – Paul Kagame

0
127

Shugaban Rwanda Paul Kagame ranar Lahadi ya bayyana cewa ƙasashen duniya sun bai wa ƙasar “kunya” lokacin kisan kiyashin da aka yi a ƙasar a 1994, a yayin da yake jawabi na tuna wa da mutanen da aka kashe shekaru 30 da suka gabata.

“Rwanda tana matuƙar ƙanƙan da kanta game da wannan bala’i. Kuma darasin da muka koya yana nan tare da mu har abada,” in ji Kagame a taron jimamin da aka gudanar a Kigali babban birnin ƙasar.

Sai dai ya ce “ƙasashen duniya sun ba mu kunya, wataƙila saboda raini ko kuma tsoro,” a yayin da yake jawabi ga ɗimbin mutane da suka haɗa da shugabannin ƙasashen duniya, da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, wanda ya ce kisan kiyashin shi ne babbar gazawar gwamnatinsa.

KU KUMA KARANTA: Kwamitin Tsaro na MƊD na buƙatar gyara – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya

Rwanda ta farfaɗo sosai a fannin tattalin arziki tun bayan kisan kiyashin, amma tana ci gaba da fama da tabonsa lamarin da ya sa ake sanya alamar tambaya game da ko da gaske mutanen da lamarin ya shafa sun yafe wa waɗanda suka yi wannan ɗanyen-aiki, wanda ƙungiyar ƴan tawayen da Kagame ta kawo ƙarshensa.

Mutane da dama suna yaba wa Kagame bisa kawo zaman lafiya a Rwanda ko da yake wasu suna sukarsa kan musguna wa ƴan hamayya.

Kamar yadda aka saba bisa al’adar kowace ranar 7 ga watan Afrilu, Shugaba Kagame ya ɗora furanni a kaburburan wasu daga cikin mutanen da aka yi wa kisan kiyashi a Maƙabartar Mutanen da Aka Yi Wa Kisan Kiyashi ta Kigali, inda aka binne sama da mutum 250,000.

Leave a Reply