Ƙasar Saudiyya ta saki ‘yan Najeriya 3 bayan tsare su tsawon watanni 10

0
250
Ƙasar Saudiyya ta saki 'yan Najeriya 3 bayan tsare su tsawon watanni 10

Ƙasar Saudiyya ta saki ‘yan Najeriya 3 bayan tsare su tsawon watanni 10

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta sanar da cewa Saudiyya ta saki wasu mata uku da ta kama a bara bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

An kama Hadiza Abba da Fatima Umate Malah da Fatima Kannai Gamboi ne tun a ranar 5 ga watan Maris ɗin 2024 a filin jirgin Mohammed bin Abdul Azeez da ke Madinah.

A cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama matan ne biyo bayan kamun wasu ‘yan Najeriya biyu da aka yi da kafso 60 na hodar ibilis wanda nauyinsu ya kai gram 900.28 da kuma wasu kafso 70 na hodar ibilis ɗin da nauyinsu ya kai gram 789.5.

“Hukumomin Saudiyya sun tsare matan ne bisa zarginsu da hannu a taimakawa wurin safarar haramtattun kayayyakin da aka samu tare da ‘yan Najeriyar da aka kama,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga

“An samu nasarar sako su ne bayan shafe tsawon lokaci ana tattaunawar diflomasiyya da shari’a, wanda hakan ya kai ga sallamarsu da kuma wanke su, da kuma mika su ga karamin ofishin jakadancin Najeriya a Jedda,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Matan sun samu tarba daga Ambasada Muazam Nayaya, jakadan Najeriya a ƙaramain ofishin jakdancin Najeriya da ke kuma inda a halin yanzu ake jiran a kammala wasu shirye-shirye waɗanda suka shafi hukumar shige da fice domin su koma Najeriya.
Ba wannan ne karo na farko da ‘yan Najeriya ke faɗawa irin wannan tarkon ba a Saudiyya.

Ko a shekarar 2019 sai da gwamnatin Najeriyar ta yi ruwa ta yi tsaki aka sako wata matashiya mai suna Zainab Aliyu wadda Saudiyyar har ta kai ga yanke mata hukuncin kisa.

Leave a Reply