Ƙasar Mali, Burkina Faso, Nijar za su ƙaddamar da sabon fasfo

0
81
Ƙasar Mali, Burkina Faso, Nijar za su ƙaddamar da sabon fasfo

Ƙasar Mali, Burkina Faso, Nijar za su ƙaddamar da sabon fasfo

Shugaban mulkin sojan ƙasar Mali, Kanal Assimi Goita, ya faɗa a ranar Lahadi cewa, nan ba da jimawa ba ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su ƙaddamar da sabbin fasfo, a daidai lokacin da ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin soja ke ƙoƙarin tabbatar da kawancensu bayan ɓallewarsu daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS.

Ƙasashen uku na yankin Sahel, waɗanda ke ƙarƙashin mulki soji, biyo bayan juyin mulki da aka fara yi tun 2020, sun haɗe ne a watan Satumbar bara a ƙarƙashin ƙawance ƙasashen Sahel (AES), bayan da suka yanke alaƙa da tsohuwar wacce ta yi musu mulkin mallaka ƙasar Faransa tare da karkata zuwa ƙasar Rasha.

Sun faɗa a cikin watan Janairun da ya wuce cewa, sun fice daga ƙungiyar ƙasashen raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, ƙungiyar da suka zarga da cewa Faransa na amfani da ita.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Mali ta dakatar da gidan talbijin na Faransa kan zargin yin ƙarya

A cikin watan Yuli, ƙawayen sun ƙulla alaƙarsu tare da kafa ƙungiyar haɗin kan yankin Sahel, wadda za ta kasance ƙarƙashin jagorancin ƙasar Mali a shekarar farko da ƙungiyar ta ƙunshi kimanin mutum miliyan 72.

Goita ya faɗa yayin wani jawabi da aka watsa ta talabijin da yammacin ranar Lahadi cewa “A cikin kwanakin masu zuwa, za’a sanya sabon fasfo na AES da nufin daidaita takardun balaguro a yankinmu.”

Ya ce “Za mu yi aiki don samar da abin da ake buƙata don karfafa cuɗanya a yankunanmu ta hanyar sufuri, hanyoyin sadarwa da fasahar sadarwa.”

Sanarwar ta zo ne kwana guda gabanin bikin cikar ƙasashen uku na cika shekara guda da kafa ƙungiyar.

Ƙasashen waɗanda makwabtan juna ne duka suna fama da rikicin masu iƙirarin jihadi da ya ɓarke a arewacin Mali a shekarar 2012 ya kuma bazu zuwa Nijar da Burkina Faso a shekarar 2015.

An yi ƙiyasin cewa rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a faɗin yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here