Ƙarin Kuɗin Lantarki: NLC ta rufe ofishin NERC

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe ofishin Hukumar Wutar Lantarki (NERC) domin nuna adawa da karin kuɗin wuta da aka yi wa ’yan Najeriya.

A safiyar Litinin jami’an NLC suka je suka rufe ofishin NERC da ke Abuja, inda shugaban ƙungiyar, Joe Ajaeronya jagoranta.

Haka ma ƙungiyar ta rufe ofishin NERC da ke Jos, fadar Jihar  Filato, inda ta hana ma’aikatan hukumar shiga ofisoshinsu domin domin gudanar da aiki.

Wakikinmu da ke Jos ya ruwaito cewa jami’an tsaro sun isa ofishin domin daƙile tashin rikici ko karya doka da oda.

Tun a ranar Lahadi ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya suka yi barazanar rufe ofisoshin NERC da na kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin Najeriya da nufin ganin an soke karin kuɗin wuta da aka yi.

KU KUMA KARANTA: Ƙarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya, ya bar baya da ƙura

Ninka kuɗin wuta da aka yi a watan Afrilu dai ya sha Allah wadai daga al’ummar Najeriya, inda daga bisani majalisar dokokin ƙasar ta ba da umarnin a soke.

NERC ta sanar da rage kuɗin da Naira 19 ga masu amfani da layin Band A waɗanda da farko ta yi wa ƙarin kuɗin kilowatt daga Naira 67 zuwa N225.

Ragin Naira 19 da NERC ta yi a makon jiya dai bai gamsar da jama’ar kasar ba.

’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa a kasar, wadda ta samo asali daga janye tallafin man fetur kafin daga bisani gwamnatin ƙasar ta janye tallafi a ɓangaren wutar lantarki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *