Ƙaramin Ministan Man Fetur na neman sasanta NNPC da Ɗangote

0
110
Ƙaramin Ministan Man Fetur na neman sasanta NNPC da Ɗangote

Ƙaramin Ministan Man Fetur na neman sasanta NNPC da Ɗangote

Heineken Lokpobiri, Ƙaramin Ministan Man Fetur, ya shiga tsakani da nufin sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin Matatar Mai ta Ɗangote da Kamfanin Mai Na Ƙasa (NNPCL).

Al’amura sun dagule a makon jiya ne, inda aka riƙa nuna wa juna yatsa tsakanin kamfanin NNPCL da mai Matatar Ɗangote kuma babban attajirin Afrika, Alhaji Aliko Ɗangote.

A wani taron ’yan jarida daya ƙira a Legas, Ɗangote ya yi zargin ƙusoshin gwamnati da kamfanonin mai na ƙasashen waje na yi wa matatarsa zagon ƙasa, ta hanyar hana ta samun ɗanyen man da za ta tace domin samar da fetur.

Bayan nan ne Farouk Ahmed, Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Ƙasa (NMDPRA), ya bayyana cewa babu kashin gaskiya a zargin da Alhaji Aliko Ɗangote ke yi.

KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya janye aniyarsa ta shiga kasuwancin sarrafa ƙarafa

Shugaban na NMDPRA ya bayyana wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Ƙasa cewa ko lasisin fara aiki Matatar Ɗangote ba ta da a shi sannan ba a kammala ta ba.

A cewarsa, matatar ba ta kai matakin kaddamarwa ba, sannan ,an dizel da take sanarwar bai kai wanda ake shigo da shi Najeriya daga ƙasashen waje ba.

Don haka ya ce Najeriya ba za ta dogara da man din Dangote ba, yana mai zargin dan kasuwan da neman kame kasuwancin ɓangaren man ƙasar shi kaɗai.

Amma a martaninsa, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce zargin ba shi da tushe, kuma idan NNPCL tana so, zai iya sayar mata da Matatar Ɗangote, ita ta gudanar da shi yadda take so.

Da hakan ta kawar da shi a matsayin mutum guda da ke neman juya aƙalar ɓangaren man.

Daga bisani, Ɗangote ya shaida wa Kwamitin Wakilai cewa man dizel ɗinsu matatar ke samarwa na da matukar inganci.

Sannan ya buƙaci majalisar ta gudanar da bincike kan zargin rashin ingancin man dizel ɗinsa domin gano gaskiya.

Wannan dambarwa da ta dabaibaye matatar mai mafi girma a Afrika kuma dunƙulalliya ta biyu mafi girma a duniya ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Musamman yadda ake tunanin matatar mai ƙarfin samar da tataccen mai ganga 650, 000 za ta taimaka wajen kawo saukin matsalar mai a Najeriya.

A kan haka ne Ƙaramin Ministan Mai, Heineken Lokpobiri, ya ƙira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin samun hadin kai da kuma shawo kan matsalar.

Masu ruwa da tsakin sun haɗa Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Dangote da Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari.

Sauran su ne Shugaban Hukumar MNDPRA, Farouk Ahmed da kuma takwaransa na Hukumar Hako Ɗanyen Mai ta ƙasa (NUPRC), Mista Gbenga Komolafe.

Leave a Reply