Ƙananan yara 2 sun mutu sakamakon nutsewa a cikin ruwa

0
212

Ƙananan yara 2 sun mutu sakamakon nutsewa a cikin ruwa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙananan yara biyu sun rasa rayukansu sakamakon nutsewa a wani ruwa da ke bayan garin Ƙofa ta Jihar Kano.

Rahotannin da Jaridar Neptune Prime ta tattara daga mutanen yankin sun ce yaran su biyar ne suka je wanka da wanki a wani ruwa da ake kira Ruwan Mai Zaure.

KU KUMA KARANTA: Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sama da 200 ya kife cikin ruwa a Neja

Bayanai sun ce Halilu Ismaʼil da abokinsa ne suka nutse a cikin ruwan, inda abokan su suka garzaya neman agaji daga kauyen Daje, amma kafin a kawo dauki, Allah ya karɓi rayuwarsu.

Arewa Updates na addu’ar Allah ya gafarta musu, ya sa su huta cikin rahamarsa.

Leave a Reply