Ƙafewar Dam a Kano, zai jawo wa masu noman rani asarar miliyoyin Naira
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Yanzu haka ɗaruruwan manoma ne ke cikin fargaba, bayan da suka zuba milyoyin kuɗinsu da niyyar yin noman rani a kewayen dam ɗin ‘yan Ganau dake ƙaramar hukumar Tsanyawa, sai dai a yanzu haka dam ɗin ya ƙafe.
Manoman waɗanda suka ce ko rijiya da suke tonawa domin ban ruwa a yanzu haka, ba sa iya taras da ruwan saboda ya yi nisa gashi kuma masu ƙaramin ƙarfi ne balle su saka a yi masu riyojin burtsatse.
A yanzu haka masara da tumatir da sauran kayan lambu na miliyoyin naira ne ke ƙonewa saboda rashin ruwa a wannan waje.
KU KUMA KARANTA:Muna ɗaukar mataki don magance rikicin manoma da makiyaya – Tinubu
Ɗaya daga cikin manoman mai suna Rahamatullahi Abdussalam, ta ce suna kallo amfanin gonakin nasu ke bushewa babu yadda suka iya.
Manoman sun ce ko a shekarar data gabata Sanatan Kano ta Arewa ya tura masu aiki zuwa dam din, amma daga karshe aikin ba’a yi shi yadda ya kamata ba.
A saboda haka manoman sunyi kira ga mahukunta a dukkanin matakai, kama daga shugaban karamar hukumar Tsanyawa da dan majalisar wakilai na Tsanyawa da Ghari da sanata Barau Jibrin da kuma gwamnan jihar Kano da su gaggauta Kai masu dauki domin ceto gonakin nasu daga bushewar da suke yi.