Zuwan Jimmy Carter Najeriya, shi ne zuwan shugaban Amurka na farko a Afirka – Dakta Hassan Gimba
Daga Ibraheem El-Tafseer
Dakta Hassan Gimba, mawallafin jaridar Neptune Prime, sannan mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan rediyon Muryar Amurka kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Jimmy Carter.
Zuwan Jimmy Carter a 1978, yana da muhimmanci ba a Najeriya ko Afirika ba, har da ita kanta Amurka ɗin. A lokacin suna neman karɓuwa a Afirka, kuma suna ganin idan Najeriya ta karɓe su, to Afirka ce ta karɓe su. Domin Najeriya ita ce shugaban Afrika.
Kafin ya zo Najeriya, akwai ɗan guntun tarihi. A da can, Najeriya da Amurka ba sa shiri, saboda abubuwa biyu. Na farko, Najeriya ba ta yafewa Amurka na goyon bayan da ta nuna wa ‘yan ɓangaren Biyafara da suke neman ɓalle wa daga Najeriya ba. Ta taimake su da makamai da duk irin gudunmawar da za ta iya ba su a matsayin ta na ƙasar Amurka.
Gwamnatin su Nixon da su Ford sun nuna son kai ga gwamnatin wariyar launin fata, wato apartheid na South Africa. Irin sannu-sannu da Amurka take yi za a ba da ‘yancin kai (Independent) a South Africa. Su Obasanjo suka nuna ba sa son jan ƙafar da ake wajen bawa South Africa ‘yanci. Suka ce a ba ta ‘yanci yanzu-yanzu kawai. Hakan ya nuna ƙarfin Najeriya da muhimmancinta.
Ba kamar yanzu ba, shugabannin Najeriya su yi ta yawo suna zuwa ƙasashen Turawa. Amma su kuma Turawan ba sa zuwa nan. Domin suna ganin babu abin da za su zo su yi a Najeriya. Hakan ya sa dole Amurka da kanta ta kawo wa shugaban Najeriya ziyara.
Kuma zuwan Jimmy Carter Najeriya, shi ne zuwan shugaban Amurka na farko a Afirka. Duk da ma kafin zuwan nasa akwai Franklin Roosevelt da ya taɓa tsaya wa a Monrovia, amma tsayawa ne kawai a hanyarsa ta wucewa. Kafin shi Andrew ma ya zo shi ya bawa Obasanjo haƙuri, ya lallaɓeshi ya kai ziyara Amurka ɗin. Ya kai ziyara sau uku.
KU KUMA KARANTA: Marigayi Jimmy Carter na Amurka ya yi tasiri a ƙulla ƙasashe abota a duniya – Masana
Sakataren harakokin wajen Amurka na wancan lokacin, ta wani wajen ma ya fi mataimakin shugaban ƙasa ƙarfin faɗa a ji. Sau uku yana so ya zo Najeriya domin a tattauna yadda za a bawa Rodesha da Namibia ‘yanci, lokacin suna ƙarƙashin South Africa, amma Najeriya ta hana shi. Wannan ya nuna ƙarfin Najeriya da kuma martaba da ta bawa kanta.