Zulum yana jefa rayuwarsa cikin hatsari don ƙarfafa gwiwar sojojin Najeriya — Badaru

0
217

Ministan Harkokin Tsaro na Najeriya Mohammed Badaru Abubakar ya yaba wa gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum kan irin goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin ƙasar ta yadda har yake saka rayuwarsa cikin hatsari ta hanyar ziyartar fagen daga don ƙarfafawa dakarun tsaro.

Da yake bayani da yabon gwamnan a fadar gwamnatin Jihar Bornin a ranar Talata, Minista Badaru ya ce “Ɗan’uwana (Zulum), da dakarun da ke Bornon da Babban Hafsan Tsaro sun ce na miƙa saƙon godiyarsu gare ka kan dukkan goyon bayan da kake bai wa sojoji.

“Kana taimaka mana a ayyukanmu, mun gode sosai. A wasu lokutan har saka rayuwarka kake yi a cikin hatsari don taimakonmu da ƙarfafa wa jami’anmu gwiwa, muna godiya,” a cewar Badaru.

Ministan ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, don duba yanayin tsaro a cibiyoyin soji na jihar Borno domin ganin an kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da aka kwashe sama da shekaru goma ana fama da su.

A nasa jawabin, Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya jaddada ƙudirinsa na ci gaba da bai wa sojojin Najeriya goyon baya a yaƙin da suke yi da ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

KU KUMA KARANTA: Boko Haram na iya shafe Najeriya idan ba a tashi tsaye ba — Zulum

“A matsayina na Gwamnan Jihar Borno, In Sha Allahu, zan ci gaba da tallafa wa sojojin Nijeriya da nufin cimma burinmu na samar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno da kuma Najeriya gaba ɗaya.

“Zan ci gaba da samar da manufofin siyasa da ake bukata don cimma wannan manufa,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayyana cewa a yanzu haka lamarin tsaro ya inganta sosai a Jihar Borno.

Kazalika Gwamna Zulum ya buƙaci sojoji da su kakkaɓe ragowar masu tayar da ƙayar baya daga dajin Sambisa da tsaunin Mandara da kuma yankunan Tafkin Chadi domin kawo ƙarshen rashin tsaro gaba ɗaya.

Gwamnan ya ƙara da cewa samun kwanciyar hankali a Tafkin Chadi zai bai wa gwamnatoci daga kowane mataki damar yin amfani da damar yin noma a yankin tafkin wajen cimma shirin samar da abinci na Shugaba Tinubu.

Leave a Reply