Zulum ya nemi goyon bayan gwamnati wajen dawo da ‘yan gudun hijirar gida
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya buƙaci gwamnatin ƙasar ta hannun Hukumar ci gaban yankin Arewa maso Gabashin ƙasar da ‘yan majalisa, su mara wa yunkurinsa baya wajen dawo da ‘yan gudun hijirar ƙasar da ke ƙasashen da ke makwabtaka da su.
Zulum ya bayyana hakan na lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban kwamitin majalisar wakilan ƙasar da ke kula da Hukumar ci gaban Yankin Arewa maso Gabashin kasar Usman Zanna, da daraktan gudanarwar hukumar Mohammed Alkali, a fadarsa da ke birnin Maiduguri.
Gwamnan ya yi bayanin cewar akwai ɗaruruwan ‘yan asalin jihar Borno da ke gudun hijira a ƙasashen Chadi da Kamaru da kuma Nijar, waɗanda ke da niyar dawowa jiharsu don ci gaba da harkokinsu na noma.
Ina rokon ku ’yan majalisa da kuma hukumar NEDC da ku tallafa wa gwamnatin jihar Borno wajen ganin an sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD
Gwamna Zulum ya ce abinda suke bukata shi ne ganin al’umma sun dogara dakansu wajen neman abinda za su ci su kuma kula da kansu.
Hare-haren mayakan Boko Haram dai sun tilasta wa daruruwan al’ummar shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya yin gudun hijira zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da su.