Zulum ya naɗa tsohon minista Bukar Tijjani a matsayin Sakataren gwamnatin jiha

Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya amince da naɗin tsohon ƙaramin ministan noma da raya karkara, Bukar Tijjani a matsayin sakataren gwamnatin jihar, (SSG).

Gwamnan ya kuma amince da sake naɗa Farfesa Isa Marte a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin sa.

Kakakin gwamnan, Isa Gusau ne ya sanar da naɗin biyu a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Laraba.

KU KUMA KARANTA: Zulum ya bada motoci ƙirar bas guda 80, da motocin ɗaukar kaya ga manoma

Isa ya ce Gwamna Zulum ya yi la’akari da irin ƙwarewar da Tijjani ya samu tun daga watan Yulin 2011 zuwa Satumba 2013 da kuma Mataimakin Sakatare-Janar kuma Mataimakin Darakta Janar, ASG/ADG, na ƙungiyar Abinci da Aikin Noma, FAO. Baya ga ofisoshin biyu, ya kuma zayyana sauran muƙaman ƙasa da sabon SSG ya riƙe a baya da suka haɗa da: National Coordinator for Nigeria’s National Programme for Agriculture and Food Security da kuma gudanar da ayyukan bankin duniya na Fadama.

Isa ya kuma ce tsohon ministan ya ziyarci ƙasashe kusan 50 domin gudanar da ayyuka daban-daban tare da bayar da gudumawa sosai wajen bunƙasa noma da samar da abinci a Najeriya da Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Tijjani mai shekaru 62, haifaffen Damasak ne, amma ya fito daga ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar. Ya halarci Makarantar Firamare ta Gubio, daga 1970–1973; Monguno Primary School daga 1967–1970 da Yerwa Government Secondary School Maiduguri, daga 1973–1978.

Yayin da yake taya sabon SSG murna, gwamnan ya buƙace shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen gudanar da ayyukan gwamnati mai inganci.

Ya kuma buƙace shi da ya mayar da hankali wajen bunƙasa ɓangarori daban-daban, musamman na noma da samar da abinci, wanda yake da masaniya a kai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *