Zulum ya buƙaci Sojoji su samar da sansani a dajin Sambisa

0
86

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya buƙaci sojojin Najeriya da su kafa sansanin soji a dajin Sambisa domin daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya yadda ya kamata.

Zulum ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da mambobin Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin soji suka kai masa ranar Laraba a Maiduguri, babban birnin jihar.

Gwamnan ya kuma buƙaci sojojin da su kafa sansanin soji a gaɓar Tafkin Chadi da kuma tsaunin Mandara wanda ke zama mafakar ‘yan ta’adda.

“Akan batun kawo ƙarshen ta’addancin gaba ɗaya, akwai buƙatar gwamnati ta kafa sansanin soji a Sambisa, gaɓar Tafkin Chadi da tsaunin Mandara.”

Ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta tabbatar da isassun kason makamai don magance matsalar tsaro.

KU KUMA KARANTA: Abin da ya sa ba a cika satar ɗalibai ba a Borno — Zulum

Zulum ya kuma bayyana buƙatar tabbatar da tsaro a Jihar Borno wadda ta yi iyaka da ƙasashe uku, musamman ta fuskar daƙile kwararowar ƙananan makamai da ke ƙara rura wutar matsalar tsaro a Arewacin ƙasar.

Ya ƙara jaddada ƙudurinsa na tallafa wa sojoji a fagen yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa kawo yanzu tubabbun ‘yan Boko Haram 190,000 ne suka miƙa wuya ga mahukunta.

A cewar Zulum, kula da ɗimbin tubabbun ‘yan Boko Haram wani ƙalubale ne da ke buƙatar goyon bayan masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply