Zuƙar tabar wiwi a tsofaffi a wuni na jinkirta musu tsufan ƙwaƙwalwa – Masana
Wasu ƙwararru a jami’ar Bonn da ke Jamus sun gano cewa shan tabar Wiwi na ƙara inganta lafiyar tsofaffi.
KU KUMA KARANTA: NDLEA a Kano ta kama tabar wiwi da kwalaben Akurkura dubu 8
Kamar yadda DW Hausa ta ruwaito, cewa tawagar ƙarƙashin jagorancin Andras Beilke-Gorzo ta gano cewar zuƙar tabar Wiwi ka iya taƙaita saurin tsufan kwakwalwa idan har waɗanda suka manyanta suna sha.









