Zawaciki: Unguwar da saurayi ke neman budurwa a ranar sallah a Kano

0
253

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hausawa suka ce ba a neman budurwa ranar sallah, saboda kowace budurwa har da ƙazama, tana caɓa ado, ta yi kwalliyar sallah. To amma a unguwar Zawaciki da ke birnin Kano ba haka abin yake ba. Domin kuwa akwai wani wuri mai tarihi da ɗaruruwan al’umma ke taruwa, sau biyu a shekara domin bukukuwan sallah. Wato sallah ƙarama da sallah babba. Kuma kowace sallah, rana ɗaya ake zuwa. Ana ƙiran wajen da Masallacin Zawaciki Idin Kwakwa.

Duk saurayin da yake so ya samu budurwa, to nan zai je, haka ma budurwar da take so ta samu saurayi to nan za ta je. Idan kuma kana da budurwa to da ita za ka je wajen. Akwai ƙauyuka da suke Kano da suke halartar wannan wuri, irinsu Gwarzo, Garun Malam, Kura da Madobi. Sannan akwai ‘yan ƙwaryar cikin birnin Kano da suke zuwa wannan waje na masallacin Zawaciki Idin Kwakwa, dake unguwar Zawaciki.

Babban abin da ake so a wannan waje shi ne saurayi ya sayawa budurwarsa Kwakwa. Wurin cika yake ya batse da jama’a hululu, samari da ‘yan mata da yara ƙanana da sauran masu son shaƙatawa sune suke cika wurin. Ana fara taro a wannan waje da zarar an idar da sallar Idi. Ana tanɗe-tanɗe da lashe-lashe a wannan waje. Sannan ƙarfe 5:00 na yamma ake korar kowa a wajen. Ana cashewa sosai a wajen, ana kaɗe-kaɗe da raye-raye sosai.

KU KUMA KARANTA: Yadda mahauci ya kashe matarsa saboda wayar hannu a Adamawa

Idan ka je wajen, za ka ga ‘yan mata ne da samari suke ta yawon kai-komo a wajen. Kowa za ka ganshi cikin farin ciki da annashuwa a wajen, musamman samari da ‘yan mata. Idan ka ga budurwar da kake so, to za ka mata magana ne. Haka ma budurwar idan ta ga saurayin da take so, to za ta yi ta nuna masa alamar tana sonsa, har sai ya gane.

To daman al’adar wajen shi ne idan ka cewa budurwa kana sonta, to dole ne ka je ka saya mata Kwakwa. Duk budurwar da ke wannan waje, babban abin da za ka burge ta da shi, shi ne ka saya mata Kwakwa. Tsire, balangu ko Yogot bai kai Kwakwa daraja ba a budurwa a wannan wajen. Duk budurwar da aka saya mata Kwakwa a wannan wajen, jin kanta take kamar ta fi kowa sa’a a duniya.

Wajen yana cika sosai, har ‘yan Kurna, Gwale, Rijiyar Lemo, Ɗorayi, Sharaɗa, Dala, Fagge da Nassarawa duk suna zuwa wajen. Sannan idan kana da budurwa za ka iya zuwa da ita wajen. Kuna zuwa kuma za ka je ka saya mata Kwakwa. Akwai waɗanda suke zuwa da iyalansu, sai su taho da taburma su shimfiɗa su zauna suna ta kallon yadda ake ta kai-komo a wannan waje. Su ma su ci, su sha su yi hani’an.

Masallacin Zawaciki Idin Kwakwa, yana nan a birnin Kano, hanyar Panshekara. An yi na ƙaramar sallah, saura na babbar sallah a nan gaba kaɗan. Duk mai so ya ganewa idonsa, to sai ya halarci na babbar sallah ɗin.

Leave a Reply