Zauren malamai ta ƙasa ta yi Allah-Wadai da matakin Gwamnatin tarayya na neman taimakon Isra’ila a ɓangaren tsaro

0
281
Zauren malamai ta ƙasa ta yi Allah-Wadai da matakin Gwamnatin tarayya na neman taimakon Isra'ila a ɓangaren tsaro

Zauren malamai ta ƙasa ta yi Allah-Wadai da matakin Gwamnatin tarayya na neman taimakon Isra’ila a ɓangaren tsaro

Daga Jameel Lawan Yakasai

Zauren majalisar malamai a Najeriya ta bayyana rashin amincewarta da yunkurin gwamnati na neman taimakon Isra’ila wajen magance matsalolin tsaro.

Zauren ya ce wannan mataki barazana ne ga ‘yancin kai, wanda zai iya haifar da cin zarafi da dogaro da ƙasashen waje, maimakon a magance matsalar daga cikin gida.

KU KUMA KARANTA: Harin da Isra’ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Zauren ya bayyana cewa bai kamata Najeriya ta jingina kanta da Isra’ila ba, musamman a lokacin da duniya ke Allah wadai da ita saboda kisan kiyashi a Falasdinu.

Taron wanda ya gudana a ranar litinin a Jihar Kano, ya sami halattar manya-manyan malamai na addini da na Boko.

Leave a Reply