No menu items!

Sample Page Title

Date:

Zargin Yunƙurin Juyin Mulkin: Ana binciken tsohon Gwamna daga kudancin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa ana binciken wani tsohon gwamna daga ɗaya daga cikin jihohin kudancin Najeriya bisa zargin alaƙa da wasu jami’an soji 16 da aka kama bisa zargin shirya juyin mulki.

Majiyoyi sun tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa tsohon gwamnan na iya zama ɗaya daga cikin masu tallafawa shirin da aka ce an tsara aiwatar da shi a ranar 25 ga Oktoba.

An ce jami’an da ake tsare da su, ciki har da Brigadier Janar da Kanal, suna aiki a Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Rundunar Sojin Najeriya sun sallami Seaman Abbas da aka tsare tsawon shekaru 6

Hukumar leken asiri ta tsaro (DIA) ce ke jagorantar binciken, tare da wakilai daga rundunonin soji uku. Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan yana da tarihi a harkar man fetur da iskar gas, kuma ana iya gayyatarsa idan aka tabbatar da hujjar haɗin kai tsakaninsa da jami’an da ake tsare da su.

Sai dai Hedkwatar Tsaron Ƙasa (DHQ) ta karyata labarin cewa akwai yunƙurin juyin mulki, tana mai cewa jami’an da aka kama ana bincikensu ne kan rashin ladabi da karya ƙa’idar aiki, ba wani shirin kifar da gwamnati ba.

Shelkwatar tsaron ta jaddada cewa rundunar sojojin Najeriya tana nan daram wajen biyayya ga kundin tsarin mulki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana kuma roƙon jama’a da su ƙaurace wa yada jita-jita.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...