Zargin Kalaman Ɓatanci: Gwamnatin Kano ta gargaɗi Malamai da su yi gum yayin da ake ci gaba da bincike

0
171
Zargin Kalaman Ɓatanci: Gwamnatin Kano ta gargaɗi Malamai da su yi gum yayin da ake ci gaba da bincike
Malam Lawal Triumph da ake zargi da kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAWW)

Zargin Kalaman Ɓatanci: Gwamnatin Kano ta gargaɗi Malamai da su yi gum yayin da ake ci gaba da bincike

Gwamnatin Jihar Kano ta gargaɗi malamai daga ciki da wajen jihar da su daina tsoma baki ko yin sharhi da zai iya kawo cikas ga aikin kwamitin shura da ke gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Abubakar Shu’aibu Triumph.

Sakataren kwamitin shura na jihar, Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Lahadi a Kano.

Sagagi ya ce gwamnatin jihar ta lura da yadda wasu malamai daga wasu jihohi ke shiga cikin al’amarin kafin kammala binciken da kwamitin ke gudanarwa.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Izala ta ƙasa ta buƙaci a sasanta dambarwar Sheikh Triumph cikin lumana

Ya bayyana cewa irin wannan tsoma baki na iya kawo tangarda ga aikin kwamitin, wanda ya ce yana gudanar da aikinsa cikin gaskiya, adalci da bin doka.

A cewarsa, “Kwamitin yana gudanar da bincike ne bisa gaskiya da adalci, don haka ya kamata kowa ya bari ya kammala aikinsa ba tare da matsin lamba daga waje ba.”

Sakataren ya kuma roƙi al’umma da sauran malamai su ba da hadin kai wajen tabbatar da cewa binciken ya gudana cikin lumana da mutunci, domin kauce wa tashin hankali ko rikici da zai iya tasowa daga batun.

Leave a Reply