Zargin ɓatanci ga Annabi (SAWW): Gwamnatin Kano ta ba da umarnin miƙawa Majalisar Shurah ƙorafe-ƙorafe kan Malam Lawan Triumph

0
369
Zargin ɓatanci ga Annabi (SAWW): Gwamnatin Kano ta ba da umarnin miƙawa Majalisar Shurah ƙorafe-ƙorafe kan Malam Lawan Triumph
Malam Lawan Triumph Kano

Zargin ɓatanci ga Annabi (SAWW): Gwamnatin Kano ta ba da umarnin miƙawa Majalisar Shurah ƙorafe-ƙorafe kan Malam Lawan Triumph

Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Majalisar Shura da ta yi nazari tare da ba da shawara kan ƙorafe-ƙorafe da suka shafi Sheikh Lawan Triumph da ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A ranar Laraba ne wasu zanga-zanga su ka yi tattaki zuwa gidan gwamnati, su na neman Gwamna da ya sa baki a lamarin.

A jawabinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci su miƙa koke-koken nasu a rubuce, ya na mai cewa zai ɗauki mataki a kai bayan sun miƙa a rubuce.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun sakataren gwamnatin jihar, Musa Tanko, ya fitar a jiya Alhamis, ya bayyana cewa gwamnati ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama daga kungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Triumph ya yi a Kano kwanan nan.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa ‘yansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawan Triumph

“Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da izinin mika ƙorafe-ƙorafen zuwa ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin ci gaba da nazari da bada shawara”

Tanko ya ce ofishin sakataren gwamnatin jihar ne ya karɓi ƙorafe-ƙorafen daga kungiyoyi kamar haka:

1. Safiyatul Islam ts Najeriya

2. Tijjaniya Youth Enlightenment Forum

3. Interfaith Parties for Peace and Development

4. Sairul Qalbi Foundation

5. Habbullah Mateen Foundation

6. Limaman Masallatan Juma’a karkashin tafiyar Qadiriyya

7. Kwamitin Malaman Sunnah na Kano

8. Multaqa Ahbab Alsufiyya

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya umurci a madadin gwamnatin jihar cewa, da a miƙa dukkan Ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa zuwa ga Majalisar Shura domin cikakken nazari da ba da shawara.

Leave a Reply