Zargin ɓullar cutar Ebola, NCDC ta tsaurara bincike a iyakokin Najeriya

0
18
Zargin ɓullar cutar Ebola, NCDC ta tsaurara bincike a iyakokin Najeriya

Zargin ɓullar cutar Ebola, NCDC ta tsaurara bincike a iyakokin Najeriya

Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya (NCDC) ta tsaurara matakan sanya idanu akan hanyoyin shigowa kasar sakamakon sabuwar barkewar cutar Ebola a Uganda.

A makon daya gabata, ma’aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da barkewar annobar da ta yi sanadiyar mutuwar mutum guda yanzu kuma take bin sawun mutane 44 da ya yi mu’amala da su.

KU KUMA KARANTA:Cutar Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Sakamakon hakan, NCDC a cikin shawarwarin data fitar tace duk da cewar babu cutar a Najeriya, amma tana aiki ne domin dakile shigowarta.

Shugaban NCDC ya bayyana cewar, “ganowa da wuri, da tsame masu fama da ita daga cikin jama’a da kirkirar dabarun tallafawa masu fama da ita su warke da kuma dabarun dakile ta a asibitoci tare da bin diddigi da sanya idanu akan mutanen da suka mu’amala da masu fama da cutar, na matukar rage yaduwarta da kuma yiyuwar mutuwa sakamakonta.”

Leave a Reply