Zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar Musulunci a Faransa

0
130

Kimanin mutum 2,000 ne suka taru a birnin Paris don nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar addinin Musulunci, da kuma cin zarafin da ƴan sanda suke yi a Faransa yayin da suke nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza waɗanda ke fama da matsala da tashin hankali na jinƙai.

Masu zanga- zangar sun riƙe tutar Falasɗinu tare da sanya ire-iren tufafi ko lullubi na ƙasar yayin da suke rera taken adawa da abubuwan da suke faruwa a Gaza a ranar Lahadi.

Kazalika sun baje alluna da ke ɗauke da rubutun “A daina nuna wariyar launin fata, a daina ƙyamar Musulunci,” “Ya’yanmu na cikin hadari,”.

KU KUMA KARANTA: Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Agadez don neman dakarun Amurka su fita daga Nijar

“A daina kisan kare dangi a Gaza” da kuma “mu na adawa da mulkin mallaka da yahudawa ke yi.”

Manya-manyan ƙungiyoyin masu ra’ayin riƙau na Yellow Vest na Faransa da kuma ‘yan jam’iyyar La France Insoumise (Faransa Unbowed) da kuma baƙaƙen mutane bakin haure ne suka halarci gangamin.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar ƴan asalin Afirka sun nuna adawarsu ta hanyar raye-raye da kaɗe-kaɗe na waƙoƙin cikin gida.

Kazalika jama’a sun rera taken tunawa da wani matashi ɗan asalin Arewacin Afirka da aka harbe har lahira a shekarar da ta gabata a yayin binciken ƴan sanda a kan hanya.

Leave a Reply