Zanga-zanga ta ɓarke akan ginin maƙabarta a Legas
Mazauna unguwar Natufe, da ke kusa da titin Babs Animashaun a yankin Bode Thomas na Surulere a jihar Legas sun mamaye tituna domin nuna adawa da shirin gina makabarta a yankin nasu.
A ranar Asabar, masu zanga-zangar, dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce kamar su: “Gwamnati ta girmama dokar CDA”, “Ku kare ‘ya’yanmu, lafiyarmu, da muhallinmu”, da kuma “Ba mu yarda a gina makabarta a ba! Gidajenmu na bukatar wataya wa, ba kaburbura ba.”
KU KUMA KARANTA: Iyaye mata sun yi zanga-zanga a Kano, saboda yawaitar faɗan daba
Masu zanga-zangar sun yi tattaki a cikin unguwar kafin su taru a wurin da ake shirin gina makabartar.
Omolabake Aminat Braimoh, shugabar Kungiyar Raya Al’umma ta Natufe/Animashaun (CDA), ta shaida wa jaridar TheCable cewa mazauna yankin tun da dadewa suka nuna adawa da wannan shiri na gina makabarta.
Ta bayyana cewa an taba kokarin fara ginin makabartar sama da shekaru biyu da suka wuce, amma al’umma suka hana ginawa.
Sai gashi an dawo da shirin yin ginin a kwanan nan, wanda ya janyo sake fitowar jama’a domin zanga-zanga.
Mazauna yankin sun ce ba za su daina nuna adawa da wannan shiri ba, ta hanyar rubuta koke-koke da kuma zanga-zanga, domin hana gina makabartar a yankinsu.









