Zanga-zanga ta ɓarke a majalisa kan harin Mauludin Kaduna

0
139

Masu zanga-zanga sun mamaye zauren majalisar dokokin tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, kan kisan bayin Allah da dama da jirgin sojoji ya yi a ranar Lahadi Legit Hausa ya wallafa.

Masu zanga-zangar sun buƙaci a yi wa waɗanda aka kashe adalci sannan sun nemi ministan tsaro, Abubakar Badaru, da ya tashi ya yi abun da ya rataya a wuyansa ko ya yi murabus, rahoton Daily Trust.

A halin da ake ciki, fiye da mutum 90 ne aka kashe a ƙauyen Tudun Biri a yankin Rigasa da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan jirgin soji ya jefa bam kan masu bikin maulidi a daren ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun ce mutum fiye da 60 ne suka jikkata a harin. Tuni rundunar soji ta ɗauki alhakin jefa bam ɗin, amma ta ƙi yin ƙarin bayani.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan soke nasarar Abba Gida-Gida (Hotuna)

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar karkashin inuwar ƙungiyar matasan Najeriya (NYCN) yankin arewa maso yamma, da ƙungiyar matasan arewa, Nasir Ishaku, ya nemi ayi wa waɗanda abun ya ritsa da su adalci, rahoton Punch.

Ya ce kisan bayin Allah ƴan Najeriya, musamman a yankin arewacin ƙasar da ake yawan yi a kullun ba abun yarda bane sannan cewa ba za a sake lamuntan hakan ba.

Ishaku ya buƙaci Majalisar dokokin tarayya da ta yi bincike kan kisan ranar Lahadi da aka yi a Kaduna sannan ta ɗauki ƙwararan mataki domin ceto ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here