Zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan soke nasarar Abba Gida-Gida (Hotuna)

An wayi gari masu zanga-zanga sun mamaye titunan Kano domin sake nuna rashin daɗinsu kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke kan gwamnan jihar.

A makonnin da suka gabata ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, inda ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na bana.

Rashin gamsuwa da hukuncin ne masu zanga-zangar tun da misalin ƙarfe takwas na safiyar wannan Larabar suka mamaye wasu manyan tituna a jihar ciki har da ƙarƙashin babbar gadar Kofar Nassarawa da titin Maiduguri daidai gadar ƙasa ta Muhammadu Buhari.

Sai dai akwai jami’an tsaro a tare da masu zanga-zangar da ke cikin shirin ko ta kwana.

Masu zanga-zangar na rera waƙoƙi da Hausa, “Ba za mu yarda ba, ba za mu yarda ba, Kano ta Abba ce, a dawo mana da hakkinmu a fallasa zaluncin kotu.”

KU KUMA KARANTA: An bankaɗo sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Aminiya ta ruwaito cewa a baya-bayan nan an yi irin wannan zanga-zangar a lokuta daban-daban a babban birnin, inda aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

A halin da ake ciki, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Kano ta gargaɗi mutane ko gungun jama’a da su guji zanga-zanga kan hukuncin kotun.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *