Zanga-zanga ta ɓarke a Senegal bayan sanar da ɗage zaɓe

0
120

Jami’an tsaron Senegal sun tarwatsa dandazon jama’a da suka taru a Dakar babban birnin ƙasar ranar Lahadi domin nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka yi, wanda a da za a yi shi ne a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaba Macky Sall ya sanar a ranar Asabar da ta gabata cewa za a jinkirta kaɗa ƙuri’ar zuwa ranar da ba a bayyana ba saboda taƙaddama kan jerin sunayen ƴan takara – matakin da jam’iyyun adawa suka yi watsi da shi.

Kimanin masu zanga-zanga 200 ne suka hana zirga-zirgar ababen hawa a babban titin birnin Dakar tare da saka shingayen na ƙonannun tayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

An kama tsohuwar Firaiministar Senegal Aminata Toure, wadda a yanzu ita ce babbar ‘yar gaba-gaba a zanga-zangar nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda ɗan majalisar jam’iyyar adawa Guy Marius Sagna ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

“Na tabbatar da cewa ‘yan Jandarma sun kama Aminata Toure,” in ji shi. Shugaban ƙasar Macky Sall ne ya naɗa Toure firaiminista amma daga baya ta koma jam’iyyar adawa.

Ƴan zanga-zangar

Ɗaruruwan magoya baya na adawa da ke zanga-zangar sun koma kan gefen titunan bayan ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaƙi mai sa hawaye. Har yanzu dai hukumomin ƙasar ba su ce komai ba kan sabon lamarin.

KU KUMA KARANTA: ECOWAS ta damu kan ɗaga zaɓen shugaban ƙasa a Senegal

Senegal dai ba ta taɓa jinkirta zaɓen shugaban ƙasa ba kuma akwai rashin tabbas kan abin da zai biyo baya.

A bara, ƙasar ta fuskanci mummunar zanga-zanga bayan da aka ɗaure jagoran ƴan adawa Ousmane Sonko, inda magoya bayansa suka ce wata dabara ce ta hana shi tsayawa takara a zaɓen.

Shekaru da dama ana kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka mafi kwanciyar hankali a tsarin dimokuraɗiyya, amma rashin ci-gaban siyasa a ƙasar ya haifar da damuwa.

Bayan sanarwar da Sall ya yi ta kafar talabijin, ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta nuna damuwa game da yanayin da ya kai ga ɗage zaben, tare da yin kira da a sanya sabuwar ranar zaɓe cikin gaggawa. An kuma buƙaci a kwantar da hankula da bin matakin sasantawa.

Leave a Reply