Zanga-zanga: Gwamnatin Yobe ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a Potiskum, Nguru da Gashuwa

0
111
Zanga-zanga: Gwamnatin Yobe ta sanya dokar hana fita na sa'o'i 24 a Potiskum, Nguru da Gashuwa

Zanga-zanga: Gwamnatin Yobe ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a Potiskum, Nguru da Gashuwa

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da kafa dokar hana fita na sa’o’i 24 a garuruwan Potiskum, Gashua da Nguru, nan take, sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankunan.

A cewar wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Birgediya Janar Ɗahiru Abdussalam (Mai Ritaya), mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro, ya ce, dokar hana fitan na nufin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garuruwan da rikicin ya shafa sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa.

Matakin na zuwa ne bayan rahotannin wasu ‘yan ɓata-gari suna amfani da damar da ake yi na zanga-zangar da ake yi suna lalata da kuma wawure kadarori na gwamnati da na al’umma.

Gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken an bi dokar hana fita ɗin, inda ta buƙaci ‘yan jihar da su kasance a gida tare da bin umarnin.

KU KUMA KARANTA: Ɗaruruwan mutane sun fito zanga-zanga a birnin tarayya Abuja (Hotuna)

Dokar hana fita za ta ci gaba da kasancewa har na tsawon sa’o’i 24, kuma an shawarci mazauna yankin da su ba jami’an tsaro haɗin kai don tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan.

Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa matakin ya zama dole domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da kuma hana ci gaba da taɓarɓarewar doka da oda.

An shawarci mazauna ƙananan hukumomin Potiskum, Gashua, da Nguru da su kasance a cikin gida kuma su guji duk wani fita da ba dole ba a lokacin dokar hana fita ɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here