Zanga-zanga: Gwamnan Kano ya roƙi Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da na lantarki

0
39
Zanga-zanga: Gwamnan Kano ya roƙi Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da na lantarki

Zanga-zanga: Gwamnan Kano ya roƙi Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da na lantarki

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta rage farashin man fetur da kuɗin wutar lantarki.

Gwamnan ya yi roƙon ne a ranar Laraba yayin ganawa da Malamai da Sarakuna da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a yayin da ake shirin fara zanga-zanga.

A cewar Gwamnan, tsadar man fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki ya haifar da damuwa ga ‘yan Najeriya wanda hakan ya sa suke shirin fita zanga-zanga.

KU KUMA KARANTA;An tarwatsa masu zanga-zanga kan ƙoƙarin kunna wuta a ƙofar gidan gwamnatin Kano

“Yakamata gwamnati ta duba ƙarin kuɗin wuta da aka yi. Wani ƙarin matsala ne ga ‘yan Najeriya. Muna ƙira ga gwamnatin tarayya ta rage farashin wanda hakan zai sauƙaƙawa ‘yan Najeriya”, inji shi.

Game da zanga zangar kuma, Gwamna Abba ya bayyana cewa duk da cewa doka ta ba da damar a yin zanga-zanga amma dole ne ta zama ta lumana.

Sannan ya ce ba zai je ko ina ba, zai tsaya ya tarbi masu zanga zangar tare da miƙa kokensu ga shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here