No menu items!

Sample Page Title

Date:

Zanga-Zanga: DSS ta musanta kai samame ofishin NLC

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta kai samame ofishin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ke Abuja a daren ranar Laraba.

Neptune Prime Hausa ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kai samame hedikwatar NLC.

A cewar ƙungiyar, jami’an tsaron sun kai samamen ne da misalin karfe 8:30 na daren Laraba.

Shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NLC, Benson Upah, ya ce, “Sun kutsa kai ne suka yi awon gaba da wasu litattafai a hawa na 2 sannan suka kwashe tarin wasu takardu.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun far wa hedikwatar NLC a Abuja

“Jami’an sun yi iƙirarin cewa suna neman kayan da aka yi amfani da su a zanga-zangar #EndBadGoveranance.”

Sai dai mai magana da yawun hukumar DSS, Dokta Peter Afunanya, yayin da yake mayar da martani, ya ce jami’an hukumar ba su kai wani samame a ofishin NLC ba.

A cewar sa, “Hukumar DSS ba ta kai samame ofishin NLC da ke Abuja ba.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...