Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

0
59
Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

A yadda ‘yan bindiga suke ta addabar jama’a a Zamfara, Sokoto da Katsina, me ya sa hukumomin tsaro ba su iya gano masu yin waɗannan ayyukan ba, sai yanzu da mutane suka fito za su yi zanga-zanga akan wahalar da ke damunsu ne suka iya bincike?”

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ƙudurinsu na soma zanga-zanga a duk faɗin ƙasar kan tsananin rayuwa da suke fuskanta, duk kuwa da gargaɗin da hukumomin tsaron ƙasar suka bayar kan yiwuwar rikiɗewarta zuwa tarzoma.

‘Yan Najeriyar da ke kukan rashin kyakkyawan shugabanci da ya haifar da ƙuncin rayuwa, tsadar abinci da kayayyaki, da kuma rashin tsaro, sun tsara gudanar da zanga-zangar lumana a duk faɗin ƙasar, domin ƙira ga gwamnati da ta sauya wasu manufofin ta da ake ganin su suka jefa ‘yan ƙasar a cikin halin da suke ciki.

To sai dai hukumomin tsaron ƙasar sun yi ta ba da gargaɗin yiwuwar rikiɗewar zanga-zangar zuwa tashin hankali.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriyar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce duk da ya ke ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka tsara, za a soma a ranar 1 ga watan Agusta, kan iya rikiɗewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a ƙasar Kenya.

KU KUMA KARANTA:Ba mu san abin da masu zanga-zanga suke buƙata ba – Gwamnonin APC

Ita ma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS, cewa ta yi ta gano wasu jagororin zanga-zangar da “manufarsu ita ce tumɓuke gwamnati.” A kan haka ta yi ƙira ga ‘yan Najeriya da su ƙauracewa shiga zanga-zangar da kuma duk wani nau’i na tashin hankali.

Ko bayan wannan kuma an ruwaito wasu gwamnonin jihohi da kuma Ministan babban birnin tarayya Abuja, suna gargaɗi tare bayyana shirinsu na hana zanga-zangar a yankunan su.

To sai dai duk da haka, wasu ‘yan Najeriyar sun dage kan cewa zanga-zanga ba gudu ba ja da baya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu ‘yan ƙasar na cewa ba wata barazana da za ta hana su ‘yancinsu na gudanar da zanga-zangar lumana, domin nuna fushinsu kan matsanancin halin da suke ciki.

Masu wannan ra’ayin na cewa duk gargaɗin da gwamnati da hukumoninta ke yi na tashin rikici sakamakon zanga-zangar, “barazana ce kawai da kuma yunƙurin kawar da hankalin ‘yan Najeriya kan mawuyacin halin da suka jefa jama’a a ciki.”

Leave a Reply