Zan tallafa wa jami’an tsaro a jihar Yobe, don ci gaban ɗorewar tsaro a jihar – Gwamna Buni

1
377

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro a jihar domin ɗorewar nasarar da aka samu kan rashin tsaro a jihar.

Gwamna Buni ya bayyana haka ne a wata takarda da babban daraktan yaɗa labarai da harkokin ‘yan jarida na gwamnan Mamman Mohammed ya fitar a yau Litinin. Ya ce Gwamna Buni ya bayyana haka ne yau a Damaturu lokacin da Manjo Janar MLD Saraso, kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta 2, Operation Haɗin Kai, da Adamu Zakari, kwamandan hukumar tsaro da tsaro ta farin kaya ta jihar suka kai masa ziyarar ban girma.

Gwamna Buni ya ce haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin tsaro tare da haɗin gwiwar al’ummomin jihar ya sa an samu gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci.

Ya ce jihar Yobe a yanzu tana zaman lafiya sosai “Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci jihar Yobe, ya kuma kwana a Damaturu a watan Janairun da ya gabata ba tare da wani ƙarin wasu matakai ko ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta ƙara ƙarfafa matakan yaƙar ambaliyar ruwa a jihar

“Ba shingayen tare hanya, ko kuma a tsayar da mota ana mata binciken ƙwaƙwaf, a tsawon zaman da ya yi a Damaturu.

“A yau kasuwanni a faɗin jihar duk a buɗe suke tare da bunƙasa harkokin tattalin arziƙi.

“Hakazalika, an gudanar da zaɓuka a cikin al’ummomin da ba za su iya gudanar da zaɓe a 2019 ba, waɗannan duk suna nuni da cewa zaman lafiya ya dawo a jihar Yobe.” Inji Gwamnan.

Buni ya yabawa shugaba Bola Tinubu, bisa ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalar rashin tsaro a dukkan sassan ƙasar nan.

Gwamnan ya kuma baiwa jami’an tsaro a jihar tabbacin ci gaba da ba da goyon baya domin samun nasarar yaƙi da duk wani nau’in miyagun laifuka a faɗin jihar.

Jami’an tsaro a jawabansu daban daban sun baiwa gwamnan tabbacin yin iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin jihar Yobe ta kasance jiha mafi aminci a Najeriya.

1 COMMENT

Leave a Reply