Zan nemi hakkina a Kotun Ƙoli – Abba Kabir Yusuf

0
182

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya ce zai garzaya Kotun Kolin Najeriya don neman hakkinsa bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da soke zaɓensa a matsayin gwamna.

Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar ga al’ummar jihar ranar Juma’a da maraice.

Ya yi jawabin ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta Kano cewa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaɓen da aka gudanar a watan Maris na 2023.

A wancan hukuncin, kotun ta cire ƙuri’a 165,663 daga ƙuri’un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa ƙuri’un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

KU KUMA KARANTA: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamnan Kano

Sai dai jim kaɗan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Kara da ke Abuja yana ƙalubalantar hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaɓen.

Amma a hukuncinta na ranar Juma’a, Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba mamba ba ne na jam’iyyar NNPP a lokacin da aka gudanar da zaɓen 2023.

Sai dai a jawabinsa ga al’ummar jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaici kan yadda Kotun ta kori ƙarar da ya kai mata.

“Abin baƙin ciki shi ne ita kanta wannan kotu ta gaba ta zauna ta kori ƙarar da muka kawo…dalilinsu guda ɗaya ne. Dalili shi ne jam’iyyar APC ta jihar Kano ta kai ƙara a kan zamana mamba na jam’iyyar NNPP,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Wannan korar ƙara da aka yi a yau muna gani ba a yi mana adalci ba. Haka kuma ba a yi wa al’ummar jihar Kano adalci ba domin mu mun sani al’ummar jihar Kano sun fito kwansu da kwarkwata sun kaɗa mana kuri’u.”

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zai garzaya Kotun Koli domin ganin ta sauya hukuncin da kotunan baya suka yanke.

“Dangane ga wannan muka yi shawara da masu ruwa da tsaki a kan cewar lauyoyinmu su shigar da wata sabuwar ƙara a Kotun Koli ta Nijeriya. Muna da yaƙini idan Allah ya yarda, wannan kotu ta karshe za ta kwato wa al’ummar jihar Kano wannan hakki nasu, haka kuma za ta kwato mana mu ma hakkinmu kuma za ta kori wancan rashin adalci da aka yi mana baki ɗaya,” a cewar gwamnan na Kano.

Leave a Reply