Zan ƙwace wuraren zubar da shara da aka mayar da su wuraren kasuwanci – Gwamnan Sakkwato

1
282

Gwamnan jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu Sokoto, ya sha alwashin ƙwato duk wuraren da ake zubar da shara da aka mayar da su harabar kasuwanci a cikin birnin.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake duba aikin kwashe shara da ake yi a dandalin Shehu kangiwa da ke cikin birnin.

Gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka mayar da wuraren zubar da shara zuwa wuraren kasuwanci, lamarin da ya ce hakan ya yi tasiri wajen tattarawa da zubar da shara a cikin birnin.

“Bari in bayyana cewa nan ba da jimawa ba, za mu ƙwato duk wuraren da ake zubar da shara da aka mayar da su wuraren kasuwanci.

“Za mu mayar da su zuwa wuraren zubar da ruwa, don sauƙaƙe da kuma inganta tattarawa da zubar da shara,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Ta kwashe tan 400 na sharar gida daga cikin birnin Kano – Hukuma

“A baya, a duk lokacin da jihar ta samu baƙo, dole ne a zaɓi hanyoyi masu tsafta don guje wa duk wani abin kunya saboda tulin ɗimbin shara da ya mamaye hanyoyinmu.

“Yanzu wannan ya zama tarihi domin mun ɗauki batun tsafta da muhimmanci.

Tun da farko, memba a kwamitin kula da tsaftar muhalli, Muhammed Toro ya ce ya zuwa yanzu kwamitin da ke kula da aikin ya kwashe sharar tireloli 1,580 a cikin babban birnin.

A wurin juji na Shehu Kangiwa, Muhammed Toro ya ce kwamitin ya yi nasarar kwashe sharar tireloli 285.

Ya ƙara da cewa shekaru huɗu ke nan da kwashe baragurbi na ƙarshe a wurin, ya kuma yabawa Gwamnan bisa kafa kwamitin da zai kula da tsaftar muhalli.

1 COMMENT

Leave a Reply