“Zamu marawa gwamnatin Yobe baya don sauƙaƙa harkokin sufiri” – Al-Wadi Travel and Tours.

0
258

Daga Sa’adatu Maina

Kamfanin sufirin jiragen sama, Al-Wadi Travel and Tours, ya ƙudiri aniyar ba da gudumawar ciyar da jihar Yobe gaba ta hanyar sufiri.

Daraktan kamfanin, Alhaji Abdullahi Muhammad Auwal ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai a sabon ofishin sa da ke kan hanyar Maidauguri a birnin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe.

Abdullahi Muhammad Auwal ya yi jawabi mai tsawo kan dalilan da suka sa ya buɗe reshen kamfanin a jihar Yobe.

Ya ce babban abin da ya sa ya kawo reshen kamfanin jihar Yobe shi ne, don sauƙaƙa mutanen jihar wajen samun biza zuwa Hajji, Umarah ko kuma tafiye-tafiye wasu ƙasashen.

Ƙari a kan wannan kuwa a cewar sa kamfanin zai ke sauƙaƙa hanyar samun biza ga ɗalibai masu sha’awar tafiya wasu ƙasashen domin karatu.

“Duba da yadda Gwamnatin jihar Yobe take ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin al’ummar jihar, akwai buƙatar mu ma ‘ya’yan jiha mu yi tamu huɓɓasar domin tallafa mata, wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka buɗe reshen Al-Wadi a nan jihar Yobe”, in ji Daraktan kamfanin.

Ya ƙara da cewa, kamfanin zai yi amfani da damar buɗe filin sauƙa da tashin jiragen sama wanda gwamnatin jihar Yobe take ƙoƙarin yi wajen bunƙasa harkokin sufiri da hada-hada a wannan yankin.

Don haka Abdullahi Muhammad Auwal ya ƙirayi al’ummar jihar Yobe da su yi amfani da wannan dama, su garzaya ofishin domin karɓar biza.

Leave a Reply