Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

0
42
Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu - NLC

Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

Daga Idris Umar, Zariya

Shugabancin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi barazanar yin watsi da duk wasu kayan aiki a duk faɗin ƙasar idan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare shugabanta, Comrade Joe Ajaero.

Kungiyar ta yi wannan barazanar ne a safiyar ranar talata a hedkwatarta, jim kaɗan bayan gudanar da taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta ƙasa, domin tattaunawa kan gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa Shugaban NLC, kan zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Hukumar ta NEC ta yanke shawarar cewa Ajaero ya mutunta gayyatar da ‘yan sanda suka yi masa amma ya lura cewa mai ba su shawara kan harkokin shari’a ya nemi ƙarin lokaci domin Shugaban NLC ya gurfana gaban hukumar ‘yan sanda.

Kwamared Ado Kabiru Sani, mataimakin shugaban ƙungiyar NLC, ya buƙaci ma’aikatan ƙasar nan da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin samun ƙarin umarni idan ‘yan sanda suka yi abin da ya saba tsammanin tsare Ajaero.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: DSS ta musanta kai samame ofishin NLC

A cewarsa “A matsayinmu na cibiyar ƙwadago, za mu mutunta gayyatar da ‘yan sanda suka yi mana, domin mu ba ƙungiyar da ba ta da fuska ba ce, amma muna aiki da lauyanmu na tsawon lokaci.

“Idan aka kama shugaban mu na ƙasa, duk ma’aikata za su sauƙe kayan aiki nan take.  Ya kamata mu jira ƙarin umarni daga shugabanninmu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here