Za mu samar da tattalin arziƙin da babu ɗan Najeriyan da zai je yana bara – Shettima

0
306

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mataimakin shugaban Najeriya ya bai wa al’ummar ƙasar tabbacin cewa sadaukarwar da suke yi, ba za ta taɓa tashi a banza ba, ya nanata cewa gwamnatinsu za ta cika alƙawurran da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan ƙasar.

Ya ce Shugaba Tinubu ya duƙufa wajen gina Nijeriya, inda kowane ɗan ƙasa ke da tabbacin tsayawa da ƙafarsa ta fuskar tattalin arziƙi, kuma inda babu wani ɗan ƙasar da zai dogara da kuɗin sadaka wajen gudanar da rayuwa.

Wata sanarwa da Sanata Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ta ambato cewa mataimakin shugaban ƙasar ya yi waɗannan kalamai ne ranar Alhamis yayin gabatar da maƙala a wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekara 63 da samun ‘yancin kai.

KU KUMA KARANTA: Mataimakin shugaban ƙasa Shettima, ya ƙaddamar da manyan ayyuka a jihar Borno

“Yau, mun haɗu a nan don karrama ƙoƙarin sake fasalin makomar Najeriya. A yau, mun kasance a kan wani matsayin tarihi mai hatsari don yin tsokaci a kan ƙasar da ta bijirewa hasashen masu mugun fata, ga wannan ƙasa da ta kasance sha-lugude.

“A tsawon sama da shekara 63, ba kawai mun iya samun bunƙasa ba ne saboda ƙudurin dukkaninmu, himmarmu ta samun ci gaba da juriya a kan aƙidar haɗin kai da ke tabbatar da zamanmu wuri ɗaya daga Aba har zuwa Ogbomosho a dangana zuwa Zariya, duk da ƙulle-ƙullen wasu tsiraru,” in ji Shettima.

Leave a Reply