Za mu nuna wa duniya cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaƙi – Erdogan

0
301

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa ƙasarsa ta soma shirin nuna wa duniya cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaƙi, a daidai lokacin da dubban mutane suke gangami da kuma nuna goyon baya ga Falasɗinu.

“A daidai lokacin da muke ɗaga muryoyinmu ga duniya muke shaida musu jin daɗinmu kan cikarmu shekara 100 da zama Jamhuriya a gobe, a yau muna magana kan abin da ke mana ciwo a zukatanmu kan Gaza,” in ji Shugaba Erdogan a lokacin da yake jawabi ga gangamin da ake yi a filin jirgin Ataturk a ranar Asabar.

Hotuna da bidiyo daga filin jirgin sun nuna mutane daga wurare da dama suna ɗauke da tutocin Turkiyya da na Falasɗinu, wasu na saka maka-wuya inda aka rubuta, “Dukkanmu Falasɗinawa ne,” “A kawo ƙarshen kisan kiyashi, a bar yara su rayu” “Sannan a zama murya ga yaran Falasɗinawa.”

“Ya Gaza da ke Falasɗinu take a 1947? Ya take a yau? Isra’ila ta ya kuka je can? Ta ya kuka shiga? Ku ‘yan mamaya ne, ku ƙungiya ce,” in ji Erdogan, inda ya bayyana cewa Turkiyya za ta gabatar da Tel Aviv ga duniya a matsayin wadda ta aikata laifukan yaƙi.

KU KUMA KARANTA: Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa

Ana gudanar da kisan kiyashi mummuna a Gaza, kamar yadda ya bayyana, inda yake ƙara tambaya kan yara da tsofaffi nawa da ba su ji ba su gani ba za a ƙara kashewa kafin a tsagaita wuta.

A yayin da yake caccakar ƙasashen Yamma kan irin goyon bayan da suka nuna wa Isra’ila da kuma yadda suka yi amfani da kafafen watsa labarai domin halatta kisan kiyashin mutanen da ba su da laifi a Gaza, Erdogan ya jaddada cewa goyon bayan Turkiyya ga Falasɗinu inda ya ce: “Isra’ila na bin ƙasashen Yamma bashi amma ba ta bin Turkiyyya. Shi ya sa muke magana ba tare da tsoro ba.”

“Littafin zunubai na ƙasashen Yamma ya sake wuce gona da iri,” kamar yadda ya ƙara da cewa, inda ya ce Isra’ila ba za ta iya aikata irin wannan zaluncin ba tare da taimakon ƙasashen Yamma ba.

‘Ba yaƙi tsakanin tsara ba ne’

Shahararren mawaƙin nan na duniya Yusuf Islam wanda aka fi sani da Cat Stevens shi ma ya yi jawabi a lokacin gangamin goyon bayan Falasɗinawa kan “tayar da bam kan iyalai da ba su ji ba su gani ba, da gidajensu musamman ƙananan yara waɗanda su ne rabin waɗanda aka kashe”.

Ya gode wa Turkiyya kan “tsayawa yadda ya kamata” dangane da halin da ake ciki a Gaza.

“Wannan ba yaƙi bane tsakanin waɗanda ƙarfi ya zo ɗaya. Idan muka kalli irin harin da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma yadda sojoji suka mayar da martani, ya wuce a yi kwatance,” in ji Islam.

Ya buƙaci ‘yan Isra’ila da su tuna abin da aka ce a cikin Attaurah: Ku tuna asalin saƙon da ubangiji ya aiko muku: Kada ku yi kisa, kada ku yi sata, kada ku nemi kayayyakin maƙwaftanku.’ Waɗannan su ne dokokin da Annabi Musa ya koya wa duniya. Me ya sa ba ku bin su?”

Tsawon makonni uku, Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare ba ƙaƙƙautawa ta sama da ƙasa kan Gaza, inda ta yi wa birnin baki ɗaya ƙawanya da kuma toshe duk wasu hanyoyi da za a shigo da abinci da fetur da magunguna.

Aƙalla Falasɗinawa 7,326 aka kashe a yayin hare-haren, inda kaso 70 cikin 100 mata ne da yara, kamar yadda alƙaluman hukumomi suka tabbatar.

A ranar Juma’a, Isra’ila ta katse hanyoyin sadarwa da na intanet a Gaza da ta mamaye, inda ta hana jama’ar birnin waɗanda ba su da yawa saduwa da sauran jama’ar duniya.

Leave a Reply